WATA BABBAR KOTUN TARAYYA DAKE ABUJA TA WANKE RT HON ALHASSAN ADO DOGUWA HARMA TA UMARCI GWAMNATIN KANO TA BIYA SHI NAIRA MILIYAN 25,BISA BATA MASA SUNA
Wata Babbar kotu dake zamanta a Birnin tarayya Abuja ta bukaci gwamnati kano data biya Rt Hon Alhassan Ado Doguwa sardaunan Rano zunzurutun kudi har Naira miliyan 25 bisa Bata suna da tayi wa Doguwa.
Akwanakin baya ne gwamnatin kano bisa jagorancin En, Abba Kabir Yusuf, gwamnatin ta sake Bude sabon shafin gurfanar da Hon Alhassan Ado Doguwa a gaban kuliya duk da kasancewar tsohuwar gwamnatin Dr Abdullahi Umar Ganduje ta APC ta wanke zargin da ake masa, yayin da bisa Dalilai na siyasa Yasa Abba k Yusuf ya sake tada maganar Alokacinda ya ke jawabi Jim Kadan bayan an rantsar dashi a matsayin Gwamnan jihar kano.
Wani bincike da mukayi na bin diddigi ya Gano cewar Hon Alhassan Ado Doguwa ya tsone idanun y'an siyasar wannan zamani bisa yunkurin sa na neman kujer kakakin majalisar wakilai na Kasa bisa cancantarsa ne Yasa makiyansa suka shiga kulle - kullen makirci irin na siyasar Kai yakai ga Nasara daga bisani Kuma Allah YA Bashi Nasara ya lashe zaben sa da rinjayen kuri, u masu yawa daga mazabar Tarayya ta Doguwa da Tudunwada, daga jihar kano.
Wasu Bata gari sunyi taron tattaunawa wato (meeting) a Abuja harma da wasu y'an jaridu da wasu kungiyoyin sa Kai da suka taka rawa wajen kulla makircin, Dan dai Kar Doguwa ya koma majalisar Kasa, Kuma Kar Yazama shugaban majalisar majalisar wakilai, Amma da yake Allah baya bacci cikin ikonsa ya kawo masa dauki ta hanyar da Bai zataba.
Y'ansanda ne suka kama Doguwa daga bisani suka gurfanar dashi agaban kotun da bata da hurumin sauraren karar, maimakon akoma da shi wajen y'an Sanda su bada belin sa sai kotun ta bada umarnin a tsare shi, daga baya wata babbar kotu ta bada belinsa.
Bayanda hukumomi suka yi kammala bincika yanzu Dai ta Tabbata Anzalinci Hon Doguwa Anyi masa kazafi tun tuni gaskiya ta bayyyana cewar wasu masharranta ne suka kulla Sharrin da ya jawo Hon Doguwa ya yi musu Allah YA Isa.
Yanzu haka Duniya ta zuba ido taga GWAMNATIN kano zata bi umarnin kotu ko kuwa!!!!
yakubu Garba
Comments
Post a Comment