BAZAN BARI AZUBAR DA JINI KO ASARAR DUKIYA BA A YANKIN KANANAN HUKUMOMIN TUDUN WADA DA DOGUWA :HON DOGUWA

 Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai natarayyar Rt Hon Alhassan Ado Doguwa sardaunan Rano (OON) yace Babu wani mutum da zai zo ya tada hankalin al, ummar karamar hukumar Tudun wada har ta Kai ga asarar rayuka da Dukiyoyin al, umma. 
      Hakan na faruwa ne adai - dai lokacin da jam, iyyar maikwando kayan gwari tazo ta samarda sharkwatar ta a kusa da sharkwatar jam, iyyar APC dake karamar hukumar Tudun wada, Wanda Wannan karara ke nuni da cewar tsokanar fada ce. 
      Hon Doguwa tare da dukkanin Magoya Bayan jam, iyyar APC yace zasu bi doka da tsari na shugaban halitta Annabi Muhammad tsira da aminci su tabbata agareshi, wajen kaucewa tada husuma ba Wai Dan anfi karfinsuba Sai Don kaucewa zubar da jinin mata da kananan Yara da matafiya da sauran al, umma. 
     Hon Doguwa tareda dukkanin yayan jam, iyyar APC na karamar hukumar Tudun wada sun gudanar da Addu, oi ciki Har da buga TABBAT YADA da sauran Addu, oi domin neman Allah ya shiga lamarin.
      Wannan manuniyace dake nuni da yadda shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai natarayyar Rt Hon Alhassan Ado Doguwa  amatsayin sa na mutum na bakwai Kuma Dattijon kasa Mai lambar (OON) ya ke kaucewa yayan jam, iyyar hamayya dake kokarin Sai ta kawo tashin hankali a kakar zabe Mai Zuwa ta 2023. 
      Doguwa yayi dogon bayani Mai ratsa zukatan yayan jam, iyyar APC yayin da yace daga yau ranar litinin 17 ga watan Oct 22 jam, iyyar APC dake da sharkwata a karamar hukumar Tudun wada da ke kusa da tashar Ingili ta koma tsohuwar sharkwatar ta ta da dake kusa da ofishin yansanda na karamar hukumar Tudun wada. 
         Rt Hon Alhassan Ado yace gamu ga ofishin yansanda ga Kuma Babban Masallachin Juma, a bakin titi duk Wanda ya taokanemu malamai da yansanda da al, ummar gari suna gani suma suzama shaida. 
        Wannan na zuwa ne adai - lokacin da kungiyoyin dake rajin kare Hakkin Dan, Adam da Kuma masu son ayi zabe cikin Lumana da Zaman lafiya Sai ga shi a Wannan Karon wasu sun fara nuni da fitsare kafarsu Dan yiwa doka Karan tsaye. 
      Hon Doguwa ya ja hankalin yayan jam, iyyar APC da cewar kada wani Dan APC yaja rigima Koda ta cacar bakice kana yakara da cewar ba sai munyi fada Allah zai bamu nasara ba me jiya tayi ballantana yau, Inji Hon Doguwa. 
        Yanzu alkalanci ya rage na al, ummar karamar hukumar Tudun wada ga Dai mutanen dake son tada zaune tsaye ga Kuma masu San Zaman lafiya. 

Comments

Popular posts from this blog

Chairman of Northern Caucus of APC Congratulates President BOLA AHMAD TINUBU and Calls for Unity and Prayer

WATA BABBAR KOTUN TARAYYA DAKE ABUJA TA WANKE RT HON ALHASSAN ADO DOGUWA HARMA TA UMARCI GWAMNATIN KANO TA BIYA SHI NAIRA MILIYAN 25,BISA BATA MASA SUNA